Ana zaben 'yan majalisar dokoki a Iran

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Hassan Rouhani na fuskantar adawa daga masu ra'ayin rikau

Al'ummar kasar Iran za su kada kuri'a don zaben 'yan Majalisun dokoki a ranar Juma'a.

Zaben zai kasance tamkar zakaran gwajin dafi na ra'ayoyin jama'a tun bayan da kasar ta cimma yarjejeniyar nukiliya da kasashen duniya.

'Yan kasar dai za zu zabi sabbin majalisu ne tare kuma da zaben kwararru da zasu kasance wakilai a majalisar da ke zaben jagoran Musulunci na kasar Iran.

Gwamnatin shugaba Hassan Rouhani na fuskantar adawa mai karfi daga masu ra'ayin rikau da ke adawa da duk wata hulda da kasashen yamma.

Tun da fari dai jagoran addini na kasar Ayatollah Ali Khameini ya yi kira ga 'yan kasar da su zabi 'yan majalisar da ba za su dinga shakkar kasashen yamma ba.

Karin bayani