'Yan kasuwar Singer sun koma shagunansu

Wasu daga cikin masu shaguna a kasuwar Singer da ke Kano sun koma kasuwar domin ci gaba da harkokinsu, bayan gobarar da suka yi.

Yawanci su suka gyara shagunan nasu ba tare da jiran alkawarin taimakon da gwamnati da 'yan siyasa suka yi musu ba.

'Yan kasuwar dai sun ce sun yi asara ta a kalla naira biliyan biyu sakamakon gobarar.

A ranar 18 ga watan Fabrairun 2016 ne aka wayi gari kasuwar ta kama da wuta tun da asubahin ranar.

Karin bayani