Nigeria: Za a kara kula da matattarar bama-bamai

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption 'Yan sanda hudu ne suka mutu sakamakon tashin bam a ofishinsu na Jimeta

Shugaban rundunar 'yan sandan Nigeria, Solomon Arase, ya umarci da a sanya matakan tsaro da kuma sa ido sosoi a kan wuraren da ake tara bama-bamai a ofisoshin hukumar.

Mista Arase ya ce an dauki wannan mataki ne sakamakon hadarin da ya faru ranar Alhamis a Jimeta Division na jihar Adamawa, domin a kiyaye faruwar hakan nan gaba.

Kazalika, shugaban 'yan sandan ya bayar da umarni ga dukkan kwamishinonin 'yan sanda da su tura jami'an kwance bama-bamai zuwa dukkan ofisoshin da ke jihohinsu domin duba matattarar bama-baman wuraren a tabbatar da ba wata matsala.

Mista Arase ya kuma mika jajensa ga iyalan wadanda suka mutu a hadarin na ranar Alhamis tare da yin kira ga al'umma su kwantar da hankulansu.

Hadarin da ya faru a matattarar bama-bamai ta Jimeta Division da ke jihar Adamawa, ya yi sanadin mutuwar 'yan sanda hudu da kuma jikkata wasu da dama.

Karin bayani