An kashe mutane tara a Somaliya

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption An kai hari a wani Otel a Mogadishu

'Yan sanda a Mogadishu babban birnin kasar Somaliya sun ce Kungiyar 'yan gwagwarmayar Islama ta kashe akalla mutane tara a yayin wani hari da suka kai a wani Otel da ke kusa da fadar shugaban kasar.

An dai ce an kashe maharan ma a yayin artabun da suka yi da masu gadin Otel din.

Rahotanni sun ce wani dan kunar bakin wake ne ya kutsa da motarsa cikin Otel din lamarin da ya bawa sauran 'yan bindigar damar bude wuta, anan ne kuma masu gadin Otel din suka mayar musu da martani.

Kungiyar 'yan gwagwarmayar Islama ta Al Shabab dai ta ce ita ta kai harin.

Har ila yau an ce an kai hari kan wani sanannan wajan shakatawa da ake kira, Peace Garden.

Iyalai da dama na zuwa wajan musamman ranar Juma'a.