An tsagaita wuta a Syria

Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Kwamitin ya bukaci gwamnatin Syria da 'yan adawa da su sake maido da tattaunawar zaman lafiya

Kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya bukaci bangarorin da ke rikici a Syria da su tabbatar sun mutunta yarjejeniyar tsagaita wuta da aka cimma da ta fara aiki.

Kwamitin ya kuma yi kira ga gwamnatin Syria da 'yan adawa da su sake maido da tattaunawar zaman lafiya a tsakanin su.

Wakilin Majalisar Dinkin Duniya na musamman a Syria Staffan De Mistura, ya ce matukar yarjejeniyar da aka cimma ta yi nasara aka kuma samu damar shigar da kayayyakin agaji, za'a fara tattaunawar sulhu a Geneva ranar 17 ga watan Maris.

Sai dai Jakadan Syria a Majalisar Dinkin Duniya Bashar al-Ja'afari ya shaida wa kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya cewa, gwamnatin Syria na da 'yancin maida martani akan duk wani farmaki da gungun 'yan ta'adda suka kai wa dakarun sojin kasar.

Babbar kungiyar 'yan adawa a Syria ta ce kusan kungiyoyin 'yan tawaye100 ne suka rattaba hannu a yarjejeniyar tsagaita wutar da gwamnati Amurka da Rasha suka yi kokarin ganin an cimma.

Sai dai Amurka ta sha alwashin ci gaba da kai wa mayakan kungiyar IS hari, yayin da Rasha ta ce ba za ta dakatar da kai hari ba akan duk wasu kungiyoyi da ta ce 'yan ta'adda ne.