Kalubale idan Birtaniya ta fita daga EU

Hakkin mallakar hoto AFP

Ministocin kudi na kasashe ashirin masu ci gaban tattalin arziki na duniya sun yi gargadin cewa tattalin arzikin duniya zai girgiza idan Birtaniya ta yanke shawarar ficewa daga kungiyar tarayyar turai a kuri'ar raba gardamar da za a yi a watan Yuni.

Kalaman na knshe a cikin wata sanarwa a karshen taron kwanaki biyu na kungiyar ta G20 a Shanghai.

Ministan kudin Birtaniya George Osborne wanda ke son ganin Birtaniya ta ci gaba da kasancewa a cikin kungiyar tarayyar turai EU ya shaidawa BBC cewa bai bukaci sanya wannan babban kalamin a sanarwar bayan taron ba.

Ministocin kundin kungiyar ta G20 sun ce farfadowar tattalin arzikin duniya ya gaza yadda suka yi tsammani a saboda haka suka yi kira ga daukar matakai na bai daya domin habaka ci gaba.