An bude kasuwar Baje Koli ta Kaduna.

Gwamnan JIhar Kaduna Nasir el Rufa'i
Image caption Gwamnan JIhar Kaduna Nasir el Rufa'i

An bude kasuwar Baje Koli ta duniya da akan gudanar kowace shekara a Kaduna da ke arewacin Najeriya

Kasuwar wacce ke ci shekara shekara na samun halartar yan Kasuwa da Kamfanoni daga sassa dabam dabam na kasar.

Sai dai a bana sabanin shekarun baya babu hada hada sosai a yayin da yan Kasuwa suka koka da rashin ciniki.

Wasu na ganin matsin tattalin arziki ne ya haifar da hakan.