Mugabe ya yi liyafar cika shekara 92

Image caption Shugaba Mugabe ya cika shekara 92 a makon da ya wuce amma sai yanzu ake yin liyafar bikin, kudin da aka kashe ya tunzura 'yan adawa.

Dubban mutane ne ke halatar liyafar murnar cika shekara 92 na Shugaban Zimbabwe, Robert Mugabe.

Ana bikin liyafar ne a kufan Zimbabwe mai tsohon tarihi da ke Masvingo a kudu maso gabashin kasar.

Ana rade-radin cewa an kashe kimanin dala 800,000 wajen shirya liyafar da 'yan adawa ke suka da cewa almubazzaranci ne, saboda farin da ake yi a kasar.

Mista Mugabe ya zama shugaban Zimbabwe ne a 1980 a lokacin da kasar ta samu 'yanci daga Britaniya.