Ba a kula da wuraren tarihi a Nigeria

Marigayi Murtala Ramat Muhammad
Image caption Wuraren tarihi na da mautuakr muhimmancim, idan an inganta su su na kawo wa kasa kudaden shiga.

Wuraren tarihin na daya daga cikin abubuwan da kan ja hankali baki 'yan kasashen waje da ke zuwa yawon bude ido.

A jihar Lagos , akwai wani waje na tarihi da aka gina wata hasumiya da ke nuna inda aka kashe tsohon shugaban Najeriya, a zamanin mulkin soje, janar Murtala Ramat Muhammad.

Sai dai duk da muhinmancin wannan waje , rashin kula ya sa mutane kan wuce wurin ba tare da sanin mahimmancinsa ba.

Ya yin wata ziyara da wakilin BBC na birnin Lagos ya kai wannan wuri, da aka gina Hasumiya da bindigogi guda biyu samfurin AK47 da aka sanya a hagu da dama, haka kuma akwai wata tukunya da taurari da takuuba har da masu.

Sai dai kuma ba kowa ke kai ziyara wurin ba, hasali ma ba a cika maida hankali a wurin ba duk kuwa da dimbin tarihin da ke tattare da wurin.