'Muna bayan Hama a Niger' —yan adawa

Hama Amadou Hakkin mallakar hoto
Image caption Hama Amadou dai ya shafe tsahon lokaci a gidan kaso.

A jamhuriyar Nijar daukacin jam'iyun siyasa na bangaren adawa sun ce za su mara wa Malam Hama Amadou baya a zaben shugaban kasar zagaye na biyu da za a yi a watan Maris.

'Yan adawan sun kuma yi fatan hukumomin kasar ta Nijar, za su saki Hama Amadou daga gidan kaso domin ya yi yakin neman zabe kamar yadda shugaba Mahamadou Isoufou zai yi.

Sai dai jam'iyar PNDS Tarayya ta ce matsalar Hama Amadou, al'amari ne na shari'a, ba ta da hannu a ciki.

Malam Hama Amadou dai Shi ne dan adawan da ya samu sama da kashi 18 cikin 100 na kuri'un da aka kada, wanda kuma zai kalubalanci shugaba Mahamadou Isoufou mai sama da kashi 48 cikin 100.