Chris Christie na bayan Trump

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Chris Christie zai marawa Trump baya

A wani lamari na ban mamaki a fafutikar yakin neman zaben shugabancin Amurka, Gwamnan jihar New Jersey Chris Christie ya bayyana goyan bayan sa ga hamshakin attajirin nan Donald Trump karkashin inuwar jam'iyyar Republican.

Mutanen biyun dai sun kasance abokan hamayya a makwanni biyu da suka gabata.

Mr Christie ya ce Donald Trump yana da damar doke Hillary Clinton, wacce ke neman tikitin tsaya wa takara a jam'iyyar Democrat.

Ya ce abu guda mafi muhimmacin ga jam'iyyar Republican shi ne ta tsayar da mutumin da zai bamu damar doke Hillary Clinton, kuma ina mai tabbatar muku cewa, mutum guda da Hillary ko kuma Bill Clinton basa son gani a wannan mataki a watan Satumba shi ne Donald Trump.

Yanzu haka dai Christie ya dakatar da yakin neman zaben sa.