An kwato garin Kumshe daga Boko Haram

Hakkin mallakar hoto AFP

Sojojin Jamhuriyar Kamaru sun ce sun yi aiki tare da dakarun Najeriya suka kori mayakan Boko Haram daga garin Kumshe da ke kan iyakar kasashen biyu.

Wani kwamandan sojin Kamarun, Janar Jacob Kodji, ya ce an kashe kimanin mayaka 100 'yan Boko Haram wajen kwato garin daga hannunsu.

Ya kuma ce an kubutar da daruruwan mutane, wadanda suka hada harda wasu 'yan mata da ake baiwa horon zama 'yan kunar-bakin-wake.

Ya ce sojojin Kamaru ukku ne aka kashe a wajen fafatawar.

Yace: "Har yanzu dakarunmu na fagen fama tare da sojojin Najeria. Mun kuma basu umurni cewa su cigaba da kai farmaki a kauyukan 'yan Boko Haram har sai mun murkushe su."