Fargabar HIV ta watsa dalibai a Sri Lanka

Yaron da ake zargi ya na dauke da cutar HIV
Image caption Ana nunawa mutanen da ke dauke da cutar HIV kyama.

Wata malama da ke koyarwa a wata makaranta da ke yammacin kasar Sri Lanka ta ce yanzu dalibi daya ne kacal ya rage a cikin dalibanta, sakamakon watsewar da sauran daliban ajin suka yi saboda zargin cewa dalibin da ya rage yana dauke da kwayar cutar HIV ko Sida.

Mahaifiyar yaron mai shekaru shida a duniya, ta shaida wa BBC cewa an fara nuna wa yaron kyama ne tun bayan rasuwar mahaifinsa, wanda shi ma a kai ta yada jita-jitar cewa cutar HIV ce ta kashe shi, alhali karya ne.

Ta kara da cewa da kyar da jibin-goshi ta samu makarantar da ta dauki yaron, bayan makarantu goma sun ki karbarsa.

Sai dai kuma a ranar farko da ya fara zuwa makarantar, iyaye suka cire dalibai daga makarantar, wadanda sun kai 186, duk kuwa da cewa Likitoci sun ba da takardar shaidar da ta tabbatar da cewa ba ya dauke da cutar HIV.