Dan India ya kashe danginsa 14

Gidan da aka kashe mutane 14 a India
Image caption Gidan da aka kashe mutane 14 a India

Wani ba'indiye ya dabbawa danginsa su 14 wuka inda ya hallakasu lokacin da da su ke barci, daga bisani kuma ya rataye kansa.

Bakwai daga cikin wadanda ya kashe yara kanana ne.

Iyayen mutumin na cikin wadanda ya kashe.

'Yan sanda sun ce makwabta su ka kira su zuwa unguwar bayan da su ka ji ihun wata mata da ke neman agaji.

Matar wadda yar uwar mutumin ce ita kadai ce ta tsira da ranta a harin.

Masu bincike sun ce watakila takardamma akan dukiya ce ta janyo kashe kashen.