Lafiyata kalau —Fati Nijar

Hakkin mallakar hoto Sani computer
Image caption Fati Nijar da Baba Ari da kuma wasu abokan aiki, a yayin daukar wani hoton bidiyon wakarta.

Binta Labaran wacce aka fi sani da Fati Nijar ta ce lafiyarta kalau ba kamar yadda ake radi-radi ba.

A hirar da ta yi da BBC, Fati ta ce ta yi wata 'yar gajeruwar rashin lafiya ta kwana daya, amma ba ta kai ga kwanciya a Asibiti ba, kuma tuni ta warke, har ta ci gaba da harkokinta.

Wani hoton bidiyo na mawakiyar kwance rai-kwa-kwai, mutu-kwa-kwai a gadon asibiti ana yi mata karin ruwa, da ake yadawa a shafukan sada zumunta da mahawara a intanet ya ja hankalin mutane da yawa.

Binta Labaran wacce aka fi sani da Fati Nijar 'yar asalin Jamhuriyar Nijar ce, ta kuma shahara a wake-waken zamani a Najeriya.

Ga hirarsu da Wakilinmu Yakubu Liman

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti