'Za mu sauya alkiblar fim' — Balaraba Ramat

Hakkin mallakar hoto Ado gidan Dabino
Image caption Labarin fim din ya kai kimanin shekaru 100 a kasar Hausa.

Mata da irin rawar da su ke takawa a mulki shi ne jigon 'Sauyin Sarauta' fim din Balaraba Ramat.

A hirar da ta yi da BBC, marubuciya kuma mai shirya fina-finai ta yi takaicin ganin cewa muna barin kyawawan al'adunmu na gargajiya musamman ta bangaren sarauta da kuma irin rawar da mata ke takawa a mulki a gidajen sarakuna.

Ganin haka ne a cewarta, ta shirya fim din 'Sauyin Sarauta' kan salon mulki da kuma gudunmawar matan sarki da sauran iyalansa wadanda ke cikin gida a wajen tafiyar da mulki a kasar Hausa kimanin shekara 100 da suka wuce.

Sannan ta kara da cewa ta kashe kimanin naira miliyan goma wajen samar da kayyakin da ake bukata na gargajiyar bahaushe ta dauri a yayin daukar fim din a kauyen Dan Hassan ta jihar Kano.

Hakkin mallakar hoto Balaraba Ramat
Image caption Naburaska da Ladin Chima a 'Juyin Sarauta'