Gwamnatin Niger na zawarcin 'yan adawa

Hakkin mallakar hoto

A Jamhuriyar Nijar, kawancen jam'iyyun siyasa da ke mulkin kasar sun ce suna tattaunawa kan yiyuwar yin kawance da wasu jam'iyyun adawa, a zagaye na biyu na zaben shugaban kasa da za ayi a wata Maris.

Daya daga cikin shugabannin jam'iyyun kawancen gwamnatin MRN, Alhaji Sala Habi, ya ce suna tattaunawa da wasu 'yan adawar, domin mara ma Shugaba Mahamadou Issoufou baya a zagaye na biyun.

Kawancen na MRN na ganin cewa goyon bayan da za su samu zai ba su damar lashe zaben ba tare da wata matsala ba.

Ikirarin nasa ya biyo bayan sanarwar da 'yan adawa suka yi na cewa za su goyi bayan dan takaran jam'iyyar Moden Lumana Malam Hama Amadou a zagaye na biyun.

Hama Amadoun ne dai dan adawan da ya zo na biyu a zagayen farko, inda ya samu sama da kashi 18 cikin 100 na kuri'un da aka kada -- hakan ne ya bashi damar kalubalantar Shugaba Isoufou, wanda ya samu sama da kashi 48 cikin 100 a karawar farko.

Karin bayani