An rataye dan sanda da ya kashe Gwamna

'Yan sandan Pakistan a bakin aiki Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Ba wannan ne karon farko da aka samu wani da yin batanci ga addinin musulunci a Pakistan ba.

A kasar Pakistan, an zartar da hukuncin kisa ta hanyar ratayewa a kan wani dan sanda, mai suna Mumtaz Qadri, wanda ya halaka wani Gwamnan lardi saboda ya kyamaci dokar hukunta wadanda suka yi batanci ga addinin musulunci.

Mumtaz Qadri dai ya harbe gwaman lardin Punjab ne da ke Islamabad, wato Salman Tasir, a shekara ta 2011.

Masu goyon bayan Mumtaz Qadri sun bazama tituna suna zanga-zanga, don nuna rashin jin dadinsu game da kisan da aka yi masa.

Tsohon gwamnan lardin dai ya yi kaurin-suna wajen sukar dokar hukunta wadanda suka yi batanci ga addinin musulunci, kuma a baya ma ya taba neman ahuwa ga wata mata Kirista, wadda aka yanke mata hukuncin kisa, saboda ta yi batanci ga addinin musulunci a wani sabanin da ta samu da wani musulmi makwabcinta.