Mun gano masu yi wa BH leken asiri —Soji

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Rundaunr sojin ta ce ba wannan ne karon farko da Moses ke yi wa Boko Haram leken asiri ba.

Rundunar sojin Najeriya ta ce ta gano wasu mutune hudu wadanda take zargi da yi wa kungiyar Boko Haram leken asiri.

Mai magana da yawun rundunar sojin kasa ta Najeriya, Kanar Sani Kukasheka Usman, ya shaida wa BBC cewa rundunar ta gano daya daga cikin mutanen, mai suna Victor Moses ne a lokacin da ya shiga wani masallaci a jihar Bauchi inda ya nemi ya musulunta.

Sai dai mutanen ba su yarda da shi ba bayan sun yi masa tambayoyi a lokacin da ya bukaci karbar shahada.

Victor Moses ya bayyana cewa shi da abokansa Salisu Muhammad Bello da Abubakar Shetima da kuma Umar Sadik Madaki suna yi wa kungiyar Boko Haram leken asiri.

Ya kara da cewar wani malami ne a Gombe ya turo su su yi leken asiri kafin a kai hari a wani masallaci na jihar Bauchi.

Kanar Kukasheka ya kara da cewa Victor Moses ya bayyana cewar ba wannan ne karo na farko da ya yi wa kungiyar Boko Haram leken asiri ba.