Badakalar lalata da yara a cocin Katolika

Fafaroma Francis
Image caption Batun lalata da yara na daga cikin abinda Fafaroma Francis ya ke kokarin magancewa a fadar Vatican.

Daya daga cikin manyan jami'anFadar Vatican ta Fafaroma Francis, George Pell na ci gaba da ba da shaida a binciken da ake yi a kan zargin lalata yara a kasar Australia.

George Pell ya ce Cocin Katolika ya tabka kura-kurai dangane da yadda ya bi kadun maganar lalata da yara da ake zargin wasu Limaman Cocin da yi.

Pell ya kara da cewa Cocin ya tabka kura-kurai, kuma yana kokarin yin gyara. Cocin ya kunyata al'umara Australia.

Jami'in ya musanta zargin da ake masa cewa ya yi kokarin boye maganar lalata da yaran lokacin da yake shugabantar reshen Cocin a Australia.