Me ke jawo cunkoso a Enugu?

Image caption Al'amarin cunkoso na addabar mutane

Cunkoson ababen hawa wata matsala ce da ke addabar masu ababen hawa a birnin Enugu, da ke kudu maso gabashin Najeriya.

Matsalar ta kan sa mutane su dauki lokaci mai tsawo ba tare da sun isa inda za su ba, ko da tazarar ba ta da nisa, musamman a kan manyan titunan birnin.

Image caption A kan shafe sa'o'i da dama cikin cunkoson motoci

Kwamandan hukumar kula da hadurra ta kasa( FRSC) a jihar Enugu, Mista David Mendie, ya alakanta matsalar da karuwar ababen hawa da yawaitar jama'a a birnin.

Yanzu haka matsalar cunkoson ababen hawa tana daga cikin matsalolin da ke addabar zinga-zirgar yau da kullum a wasu manyan biranen Nijeriya, kamar su Legas da Abuja da Kano da Fatakwal da sauransu.

Karin bayani