Erdogan zai kai ziyara Ghana

Racep Tayyep Erdogan Hakkin mallakar hoto no credit
Image caption Kulla huldar kasuwanci na daga cikin dalilan kawo ziyarar.

A yau ne ake sa ran Shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan zai gabatar da jawabi a gaban majalisar dokoki ta Ghana.

Jiya ne dai Mista Erdogan ya isa kasar ta Ghana daga Ivory Coast a ci gaba da wata ziyara ta mako guda a wasu kasashen Yammacin Afirka.

Ziyarar shugaban na Turkiyya za kuma ta kai shi Najeriya da Guinea.

Ana sa ran a jawabin nasa ga majalisar dokoki ta Ghana, Mista Erdogan zai tabo batutuwan da suka shafi dangantakar kasashen biyu da yadda za su amfana da juna.

Irbad Ibrahim wani mai sharhi a kan al'amuran yau da kullum a kasar ta Ghana, ya kuma shaidawa BBC cewa wannan ziyara na da matukar muhimmanci ga kasar ta fuskar tattalin arziki da sauransu.