Namiji ya lashe gasar fasaha ta `Girls in tech`

Hakkin mallakar hoto thinkstock
Image caption Gasar Girls in tech ta zama ta maza da mata

Kamfanin fasahar makamashi na EDF Energy na shan suka bayan wani yaro dan shekara 13 da haihuwa ya lashe wata gasar da aka tsara da nufin kwadaita wa mata nazari a fannonin kimiyya da fasaha da kuma lissafi.

An dai bukaci yara ne da su yi amfani da basirarsu wajen samar da hanyoyin tallata kayan daki.

Sai dai kamfanin ya ce duk da cewa an tsara gasar ne don yara mata, an ba wa maza 'yan shekara 11 zuwa 16 da ke Birtaniya damar shiga gasar.

BBC dai ta fahinci cewa na yanke shawarar bude gasar ga jinsin maza da mata ne da nufin kamanta adalci ga kowa da kowa, kuma daruruwan yara sun shiga gasar.

Bayan an gudanar da gasar har sau uku a Birtaniya a bara, sai aka ba da damar shiga gasar ta intanet, kuma a lokacin ne aka ba wa maza damar shiga.