An kama mace dauke da ƙoƙon kai

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption 'Yan sanda sun yi wa matar karfa-karfa.

'Yan sanda a birnin Moscow sun cafke wata mata, bayan da aka gano tana dauke da ƙoƙon kan wani yaro da aka datse.

Wani faifan bodiyo ya nuna matar na tafiya kusa da wani ofishin 'yan sanda.

'Yan sandan sun yi mata ƙarfa-ƙarfa suka kayar da ita, kuma yanzu haka likitocin lura da masu tabin-hankali na duba lafiyarta.

Ana zaton matar ta je Moscow ne daga yankin tsakiyar Asiya, kuma mai rainon yaron da aka datse wa kan ce.

An zarge ta da kashe yaron ne kafin ta bankawa gidan iyayensa wuta a arewa maso yammacin birnin Moscow.

An kuma gano gangar jikin yaron mai shekaru hudu a can.