An rataye mutumin da ya kashe gwamna a Pakistan

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption An baza jami'an tsaro a garin Qadri domin tunkarar duk wani da ke shirin tayar da rikici.

Hukumomi a kasar Pakistan wani tsohon jami'in da ke tsaron lafiyar gwamna jihar Punjab, wanda ya harbe gwamnan har lahira.

Mumtaz Qadri ya kashe Gwamna Salman Taseer a birnin Islamabad a shekarar 2011, lamarin da ya girgiza 'yan kasar.

Gwamnan yana adawa da dokokin yin ridda.

Wasu kungiyoyin da ke ikirarin kishin Musulinci sun yaba masa, yana mai bayyan shi a matsayin "gwarzo", sannan dubban masu tsattsauran ra'ayi ne suka yi zanga-zangar nuna goyon bayansa a lokacin.

Mutane da dama sun yi zanga-zanga bayan samun labarin rataye shi.

An sanya jami'an tsaro a cikin shirin ko-ta-kwana, sannan an kara jami'an 'yan sanda a garin su Qadri da ke kusa da Islamabad.