An sake tsare jagoran 'yan hamayya a Uganda

Hakkin mallakar hoto AP

'Yan sanda a Uganda sun kuma tsare jagoran 'yan hamayyar kasar, Kizza Besigye, a lokacin da ya yi kokarin barin gidansa, kwanaki 10 bayan da aka yi masa daurin talala a karo na farko.

'Yan sandan sun kuma fitar da wasu 'yan jarida guda biyu daga wurin da lamarin ya auku.

An sha kama Mista Besigye a lokuta da dama tun bayan zaben shugaban kasa a farkon wannan watan wanda ya zo na biyu Yoweri Museveni, wanda ya shafe shekaru 30 yana mulkin Uganda.

Mista Museveni ya zarge shi da kitsa rikici.

Mista Besigye ya yi Allah wadai da zaben inda ya ce an yi magudi.