Motar Google marar matuki ta yi hadari

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Motar Google marar matuki

Wata mota mai tuka kanta da kamfanin fasaha na Google ya kera ta ci karo da wata motar safa lokacin da take tukin gwaji a birnin California.

Wannan dai shi ne karon farko da mota marar matukin ta yi hadari a kan babban titi.

Wakilin BBC ya ce mota marar matukin na tafiyar kilomita uku ne a cikin sa'a guda lokacin da ta gwara da maotar safa mai tafiyar kilomita 24 a cikin sa'a daya. Kuma na'urar motar mai lura hanya ta yi zaton motar safan ta tsaya ne, don haka mota marar matukin ba ta saurara ba.

Wani binciken da aka gudanar ya nuna cewa motar ta yi hadarin ne a kusa da hedikwatar kamfanin Google din da ke Mountain View, tun makwanni biyu da suka shige.

Babu dai wanda ya jikkata, kuma kamfanin ya dauki alhakin hadarin, ya kuma dukufa wajen yin wasu gyare-gyare ga manhajar da ke sarrafa mota marar matukin.