Artabu tsakanin 'yan sanda da 'yan cirani a Calais

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Matakin da aka dauka a kan 'yan ci-ranin dai bai yi wa hukumar da ke kula da 'yan ci-rani dadi ba.

An ci gaba da yin artabu da 'yan ci-rani a sansanin 'yan share-wuri-zauna da ke Calais a bakin ruwan Faransa, wadanda ke yunkurin isa Birtaniya, a lokacin da ake rusa daruruwan bukkokinsu.

'Yan sanda kwantar da tarzoma sun fesa wa wasu daga cikin 'yan ci-ranin barkonon-tsohuwa, wadanda ke jifar 'yan sandan da duwatsu.

Haka dai aka yi ta dauki-ba-dadi da gungun wasu 'yan ci-ranin, wadanda suka bazama kan titin da ya nufi tashar jiragen ruwa.

Wannan matakin da aka dauka a kan 'yan ci-ranin dai bai yi wa hukumar da ke kula da 'yan ci-rani dadi ba.

Leonard Doyle, shi ne Jami'in sadarwa na hukumar ya kumace akwai kudurce-kudurcen Majalisar Dinkin Duniya da dama da suka wajibta mutunta 'yan ci-rani, kuma kada A manta da cewa mutane ne da ke gudun-hijira ko neman mafaka.

Mahukunta dai sun bukaci 'yan ci-ranin su koma cikin wata kwantaina da aka girke a gefe, amma wasu daga cikinsu na fargabar shiga, saboda yin haka zai bukaci karbar mafaka a Faransa, sabanin burin da suke da shi na zuwa Birtaniya.