Zika ka iya janyo cutar shanyewar jiki

Jaririn da aka haifa da cutar Zika Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Baya ga tawayar da ake haifar jarirai da su, cutar Zika na haddasawa yara zama gaula.

Wani sabon bincike ya gano cewa cutar Zika za ta iya haddasa mummunar rashin lafiyar da ke shafar jijiyoyin jiki, wadda a karshe ka iya zama sanadin shanyewar jiki.

Masu binciken sun yi nazarin wasu mutane ne da suka kamu da cutar Zika lokacin da annobarta ta barke a Polynesia ta kasar Faransa, shekaru biyun da suka wuce.

A cikin sakamakon binciken, masana sun ce ana iya samun mutum guda daga cikin mutum 4000 da suka kamu da cutar Zika, wanda a karshe ke samun larurar shanyewar jiki, lamarin da ka iya zama sanadin mutuwa.

Sauro ne dai ke yada cutar Zika, kuma ana danganta ta da wata tawayar da jirirai ke samu a kwakwalwarsu.