Yunkurin tsige Zuma daga mulki

Hakkin mallakar hoto

Wata kotu a Afrika ta kudu za ta saurari karar da 'yan hamayya suka shigar kan tuhume-tuhume 738 a kan Shugaba Jacob Zuma.

Sai dai ofishin shugaban kasar ya ce zai yi adawa da matakin saboda masu shigar da kara sun yi abin da ya dace a lokacin da aka wanke shi daga zarge-zargen da ake masa a shekarar 2009.

'Yan hamayya sun yi amannar cewa akwai siyasa a cikin al'amarin kuma hakan ne ya bude wa Mista Zuma hanyar zama shugaban kasa.

An yi zargin ya karbi cin hanci a kan wani shiri na sayen makamai, wanda darajarsu ta kai biliyoyin dala, sai dai shugaban ya musanta zargin.

A lokacin, hukumar da ke kula da shigar da kara ta kasa, NPA, ta ce wasu shaidu da aka nada ta wayar tarho, sun nuna cewa wasu sun yi kokarin yin katsalandan a cikin binciken.

Babbar jam'iyyar adawa ta Democratic Alliance za ta kalubalanci shawarar da kotin kolun ta yanke bayan an shafe kusan wata shida ana fafatawa.