An fara kada kuri'a a jihohi 11 na Amurka

Hakkin mallakar hoto Getty

An fara kada kuri'a zaben fidda gwani mafi girma ga 'yan takarar shugabancin Amurka karkashin manyan jam'iyyun kasar biyu.

Jihohi 11 ne za su zabi gwaninsu daga cikin 'yan takarar.

Dan takarar jam'iyyar Republican Donald Trump na fatan ya ci gaba da rike tagomashinsa da ya samu a zabukan da aka yi a baya.

Shi kuwa abokin karawarsa a jam'iyyar Sanata Ted Cruz, na kokarin ganin ya samu nasara a jiharsa ta haihuwa Texas, domin ya doke Mista Trump.

A bangaren 'yan jam'iyyar Democrat kuwa, Hillary Clinton ce ke son ta samu nasara kan Bernie Sanders, dan takara mai ra'ayin gurguzu wanda yake samun kuri'un matasa.

A ranar 8 ga watan Nuwamba ne za a zabi sabon shugaban Amurka da zai maye gurbin Barack Obama.