Arzikin Dangote ya kara habaka

Aliko Dangote ne ya fi kowa kudi a nahiyar Afrika
Bayanan hoto,

Aliko Dangote ne ya fi kowa kudi a nahiyar Afrika

Arzikin mutumin da ya fi kowa kudi a Afrika Aliko Dangote, ya kara habaka da dala biliyan 15.4.

An bayyana hakan ne cikin jerin wadanda suka fi arziki a duniya da mujallar Forbes ta wallafa.

Dangote ya zama na 51 cikin jerin wadanda suka fi kudi a duniya idan aka kwatanta da na bara da zama na 67, a lokacin da mujallar ta kiyasta yawan dukiyarsa cewa ta kai dala biliyan 14.7.

Shi ne mamallakin kamfanin siminti mafi girma a Afrika wato Dangote Cement.

Mutum na biyu da ya fi kowa arziki a Afrika ma dan Najeriya ne Mike Adenuga, wanda ya mallaki dala biliyan 10.

Nicky Oppenheimer, dan kasar Afrika ta kudu shi ne na uku a jerin mutanen da suka fi kudi a Afrika, inda ya mallaki dala biliyan 6.6.

Mujallar ta sanya Mista Adenuga na 103 a jerin wadanda suka fi kudi a duniya, shi kuma Mista Oppenheimer ya zama na 174.