An kona masu amfani da kasusuwan zabiya

Image caption Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadi cewa zabiya mutum ne kamar kowa

An kona wasu mutane bakwai kurmus a Malawi bayan an yi zargin kama su dauke da kasusuwan bil adama.

'Yan sanda sun ce wasu mutane ne suka kwarawa mutanen man fetur ya kuma cinna musu wuta a wani kauye da ke nesa da kudancin kasar.

An yi amanna cewar kasusuwan na zabiya ne.

Wasu sun yi amanna cewar tsafi da bangarorin jikin zabiya na kawo sa'a a rayuwa.

Majalisar Dinkin Duniya ta ce an kashe zabiya guda tara a Malawi cikin shekara guda da ta gabata.

A kasashen da ke makwabtaka da Malawi ma kamar Mozambik da Tanzaniya ana amfani da bangarorin jikin zabiya don yin tsafi.

Karin bayani