'Ana bin Nigeria bashin $64 biliyan'

Sanata Shehu Sani
Image caption Sanata Shehu Sani ya ce jihohi da dama a Nigeria sun karbi bashin daya fi karfin su

Majalisar dattawan Nigeria ta ce yawan bashin da ake bin kasar ya kai dala biliyan sittin da hudu.

A wata hira da BBC, shugaban kwamitin kula da basussuka na Majalisar dattawan Najeriya Sanata Shehu Sani ya ce daga cikin bashin da ake bin kasar, kimanin dala biliyan 10 da miliyan 600 bashi ne da aka karbo daga kasashen waje, yayin da sauran kuma basussuka ne na ciki gida da ake bin gwamnatin tarayya da jihohi da kuma kananan hukumomi na kasar.

Sanata Shehu Sani ya ce mafi yawan kudade bashi ne da aka karba a shekarun baya, kuma jihohi da dama a Nigeria sun karbi bashin daya fi karfin su.

Ya kara da cewa za'a shafe nan da shekaru hamshin kafin kasar ta iya biyan basussukan da ake bin ta.

Rahotanni sun ambato wani jami'in bankin Musulunci na Islamic Development Bank na cewa Najeriya na kashe kusan kashi tamanin cikin dari na kudaden shigar ta wajen biyan kudaden ruwa na basussukan da ta ciyo a baya.