'Yan sanda sun mika Ese ga iyayenta

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Sarkin Kano ya ce tun watanni shida da suka gabata ya mika Ese ga rundunar 'yan sandan jihar

Hukumar 'yan sandan Nigeria ta mika yarinyar nan da ake zargin wani saurayi ya sato ta daga jihar Bayelsa ya kuma kai ta jihar Kano ga iyayenta.

Wannan batun dai ya janyo cece-ku-ce a kasar, musamman a dandalin sada zumuta da muharawa a intanet.

Jiya ne aka shirya mika yarinyar ga iyayenta a shalkwatar 'yan sandar kasar amma hakan bai yi wu ba.

A cewar kakakin rundunar 'yan sandan ta Najeriya, Olabisi Kolawole, ba za su kyale saurayin ba da ma duk wani wani jami'in 'yan sanda da aka samu da ba daidai ba a maganar tun asalinta.

Sai dai kuma 'yan sandan ba su bai wa kowa damar tattaunawa da yarinyar ko iyayenta ba.

Ga dai rahoton da Yakubu Liman wanda ya halarci taron ya hada mana.

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti