'Yan Nigeria sun sake kai karar Shell

Hakkin mallakar hoto Reuters

An kai karar kamfanin mai na Shell a wata kotun London a karo na biyu a cikin shekara biyar a kan gurbatar muhalli a yankin Niger Delta na Najeriya.

Al'umomi biyu ne suka kai karar, suna neman diyya daga wurin Shell, sannan suna so ya tsaftace musu muhallinsu.

Shell ya ce yana matakin farko a nazarin da yake yi a kan karar da aka shigar a kansa kuma yana so a saurari karar a Najeriya.

Al'ummar Ogale mai yawan mutane dubu 40 a jihar River ta gabar tekun Najeriya, wadanda akasarinsu manoma ne da masunta, suna daga cikin wadanda suka shigar da karar.

Lauyoyin Leigh Day ne ke jagorantar shari'ar.

A karar da al'ummar ta shigar ta ce gurbatar muhallansu tun shekarar 1989 ta sa al'ummar tana fama da rashin ruwan sha mai kyau da lalacewar gonaki da koguna.

Wannan malalar mai, ita ce musababbin kara ta baya-bayan nan da al'ummomin yankin suka shigar da reshen kamfanin Shell a Najeriya.

An dai shafe shekaru da dama ana fama da matsalar malalar mai a yankin Neja Delta, kuma kungiyoyin kare Hakkin Bil-Adama sun zargi kamfanonin man da gazawa wajen tsabtace muhalli.

A bara Shell din ya amince da wata 'yarjejeniya a wajen kotu inda ya biya fiye da dala miliyan 80 a matsayin diyya ga al'ummar Bodo, sakamakon malalar mai a 2008.

Za'a dai shafe shekaru da dama ana tafka wannan sharia, amma ko yaya hukuncin ya kasance, shari'ar ta sake janyo hankalin duniya a kan yadda wani katafaren kamfanin mai ya ke tafiyar da ayyukan sa wajen kare muhalli