'Yan jam'iyyar Republican na sukar Donald Trump

Hakkin mallakar hoto
Image caption 'Yan jam'iyyar Republican na sukar Trump

Manyan 'yan jam'iyyar Republican sun kara matsa kaimi wajen sukar Donald Trump bayan da ya rike matsayinsa a matsayin wanda ga alamu shi ne zai yiwa jam'iyyar takarar shugabancin kasar Amurka.

Mr Trump ya lashe jihohi bakwai a fafatawar da akayi a ranar Talata inda sanata Ted Cruz ya samu jihohi uku.

Sanata Lindsey Graham mai wakiltar South Carolina ya ce hanya guda da za a bi a shawo kan Donald Trump ita ce a kara assasa yakin neman zaben Ted Cruz, amma kuma ya ce ba shi da tabbas a kan ko yin hakan zai sa a dace.

A ranar Alhamis ne tsohon dan takarar shugabancin kasa karkashin jam'iyyar Republican Mitt Romney zai yi jawabi inda ake kyautata zaton zai kalubalanci Mr Trump.