EBay, Amazon da Google sun goyi bayan Apple

Hakkin mallakar hoto Getty

Manyan kamfanoni da suka hadar da eBay da Google da kuma Amazon sun bi sahun Twitter da AirBnB wajen goyon bayan kamfanin Apple a shari'ar sa da yake da Hukumar FBI.

Hukumar ta FBI dai na bukatar Apple da ya taimaka wajen bude wayar wani da ake zargi da hallaka mutane goma sha hudu a California a bara wato Syed Rizwan Farook.

Farook da matarsa sun kashe mutane goma sha hudu a California a watan Disambar da ya gabata.

Tuni dai iyalan wadanda aka kashen suka goyi bayan hukumar ta FBI a kan wannan bukata.

Kamfani Apple dai ya ce babu wata kotu da ta taba tilasta wa kamfanin rage matakan kariya a kan kayayyakin da kamfanin ke sayar wa don samun damar binciken bayanan wani da ke amfani da wayar kamfanin.

Dan haka Apple ya ce hukumomin tsaro na neman a ba su iko mai hadari kuma yin hakan ya saba wa doka.