'Ba za mu kai labari ba' —Bilic

Kociyan West Ham Slaven Bilic na jin cewa kulob din su ba zai labari a gasar zakarun Turai ba.

Kulob din na mataki na 6 a gasar, kuma da maki 1 a bayan Manchester wacce ta ke ta 4 bayan da Manchester ta doke Tottenham 1 da 0 a ranar Laraba.

An rawaito Bilic na cewa "kai wa ga nasara abu ne mai wuya, sai dai babu laifi mu ci gaba da kokari".

Kociyan ya ci gaba da cewa zai sa wannan cikin kudirin kulob din ganin cewa sun koma sabon filin wasa, ga karin kudin shiga da magoya baya da kuma girman kulob din.