Manhajar auna jini bata bayar da sakamakon gaskiya

Hakkin mallakar hoto Thinkstock
Image caption Manhajar auna jini bata bayar da sakamakon gaskiya

Masu bincike a Amurka sun ce manhajar nan ta wayar tafi da gidanka da ta yi fice wadda kuma aka kirkiro don auna yadda jinin mutum ke tafiya a cikin jiki, bata bada sakamako na gaskiya game da halin lafiyar masu amfani da ita.

Manhajar mai suna Instant Blood Pressure, na ikirarin cewa mutum zai iya auna jinin sa ta hanyar ajiye wayar tafi da gidanka a kirjin sa tare da sanya dan yatsansa a jikin Camerar da ke jikin wayar.

Sai dai wani bincike da aka wallafa a mujallar kiwon lafiya ta kungiyar likitoci a Amurka, ya ce an samu kuskure a awon jinin mutane 8 daga cikin mutane 10 da aka auna jinin su da manhajar, lamarin da ya jefa rayukan masu amfani da manhajar cikin hadari.

Fiye da mutane dubu dari ne dai suka sauke manhajar a wayoyin su don amfani da ita.