'Kungiyar LRA ta sace mutum fiye da 200'

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Joseph Kony ya yi kaurin-suna wajen kashe mutane.

Wata kungiya da ke sa ido a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya ta ce 'yan tawayen LRA sun sace fiye da mutum 200 da suka hada da kananan yara 54 a hare-haren da suka matsa kai wa a 'yan makwannin nan.

Rahoton da kungiyar ta fitar kan rikicin da madugun kungiyar, Joseph Kony, ya jagoranta ya ce mai yiwuwa 'yan tawayen sun tilasta wa kananan yara shiga aikin soja, da yin lalata da kuma bautar da su.

Kungiyar Crisis Tracker ta ce mayakan LRA sun sace mutane da yawan su ya rubanya adadin mutanen da suka sace a baya-bayan nan a yankin a shekarar 2015.