An ragewa Janar Ransome-Kuti mukami

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption A watan Janairun 2015 ne, kungiyar Boko Haram ta kai hari Baga

Majalisar koli ta rundunar sojin Nigeria, ta tabbatar da tuhumar da kotun soji ta musamman take yi wa Birgediya Janar Onitan Ransome-Kuti.

Sai dai majalisar ta sauya hukuncin da aka yanke masa tun farko na kora daga aiki zuwa rage masa mukami daga Birgediya Janar zuwa Kanal.

Hukumar ta kuma dauke masa hukuncin daurin wata shida a gidan yari da aka yanke masa tun farko ta kuma wanke shi tas.

An yankewa Janar Ransome-Kuti wannan hukunci ne a watan Oktobar 2015, saboda zarginsa da sakaci a harin da Boko Haram ta kai garin Baga a jihar Borno a watan Janairun 2015 din.

Karin bayani