'Nigeria ce ta biyu wajen mutuwar mata da jarirai'

Hakkin mallakar hoto
Image caption Za'a rika yi wa mata masu juna biyu gwajin ciki kyauta a yankunan karkara.

Gwamnatin Najeriya ta ce akalla mata dubu 33 da kuma jarirai dubu 240 ne ke mutuwa a kowace shekara a kasar sakamakon matsalolin da mata ke cin karo da su wajen haihuwa.

Da yake jawabi yayin kaddamar da wata sabuwar na'urar tafi da gidanka da ke iya nuna halin da mace mai ciki da abin ke cikinta ke ciki na take, karamin ministan lafiya na kasar Dr. Osagie Enahire ya ce wannan ya sa kasar ke zaman ta biyu a yawan mace-macen mata da jarirai a duniya.

Gwamnatocin Amurka da Najeriyar ne dai suka dauki nauyin samar da na'urorin domin fadada hanyoyin samun kulawa ga mata masu juna biyu a kasar.

A hira da ya yi da BBC, shugaban hukumar kiwon lafiya a matakin farko a Najeriya Dr. Ado Muhammad ya ce za a rarraba na'urorin ne ga ungozomomi domin rika yi wa mata masu juna biyu musamman a yankunan karkara gwaje-gwaje kyauta.