Fitattun masu amfani da shafukan zumunta a Saudiyya

Image caption Wasu daga cikin 'yan Saudiyya da ake bi a shafin Twitter

Ba abin mamaki ba ne da malaman addini suka shahara a wajen amfani da shafukan sada zumunta a kasar Saudiyya, ganin cewa kasar ita ce "jagorar Musulmai da duniya".

Sai dai wannan shahara da suka yi cike take da kalubale. Don haka, su wanene wadannan malaman addini wadanda suka shahara tamkar fitattun mawaka da manyan shugabannin duniya

Kuma me suke wallafa wa a shafukan intanet? A wannan shiri na musamman da BBC ta yi wa take: ''Yan Saudiyya da ke amfani da shafukan zumunta: Addininsu, da 'yancinsu da kuma yanayin walwalarsu", mun duba shafukan Twitta hudu

da suka fi shahara a kasar.

1. Mohammad Al-Arifi
Image caption Mohamed Al-Arifi: Malami ne mai janyo cece-kuce.

Mohamed Al-Arifi shi ne kan gaba a cikin malaman addinin Islama na Saudiyya da ma duniyar Musulmai da ke da kwarjini, sai dai mutum ne da ke janyo cece-kuce.

Wasu daga cikin ra'ayiyoinsa a kan mata na cike da rudani. A shekarar 2007 lokacin da yake jawabi a wani shirin talabijin, Al-Arifi ya gaya wa maza cewa za su "iya dukan matansu idan suka ki yi musu biyayya amma ba duka mai tsanani ba."

Haka kuma a shekarar 2012, Al-Arifi ya wallafa a shafinsa na Twitta cewa bai kamata a bar mata suna fita daga gidajensu suna zuwa aiki ba.

Al-Arifi yana da kyakkyawar dangantaka da gwamnatin Saudiyya da kuma gidan Sarautar kasar, ko da ya ke wasu lokutan suna samun rashin jituwa.

A shekarar 2014, an tsare Al-Arifi a kasar ta Saudiyya na wani karamin lokaci bayan ya soki wani kamfanin gina layin jirgin kasa kan wani titi da ya yi da ya hada wurare masu tsarki na kasar, yana mai cewa titin shi ne mafi muni a duniya.

Baya ga al'amuran yau da kullum, Al-Arifi yana bayyana ra'ayoyi a kan siyasa a yankin Gabas ta tsakiya.

Image caption Fassara: “Kamfanonin jiragen saman Saudiyya sun ki daukar mata aikin hidima a cikin jirgi. Na gode musu kuma ina fatan za su dauki maza ne zalla su kuma ci gaba da kin daukar mata.”

Ya yi kaurin-suna wajen kyamar 'yan Shia kuma an zarge shi da kokarin haddasa husuma bayan an rawaito shi yana bayyana 'yan Shia a matsayin "kafirai, wadanda ya kamata a kashe.".

Ra'ayinsa kan 'yan kungiyar IS yana da harshen-damo.

A wata huduba da ya gabatar a kasar Masar a shekarar 2014, Al-Arifi ya yi kira da a yaki shugaban Syria Bashar Al-Assad, ko da ya ke bai fito fili ya bayyana abin da yake nufi ba.

A shekarar ne kuma aka hana shi shiga Biritaniya bayan ya yi wa'azi a wani gari Cardiff, wanda wasu samari guda uku da suka tafi Syria domin goyon bayan IS suka halarta. Da yake mayar da martini kan hana shi shiga Biritaniya, Al-Arifi ya wallafa a shafinsa na intanet cewa yana "matukar adawa da hanyoyin da masu tsattsauran kishin addini" ke bi wajen cimma burinsu.

2. Ahmed Al-Shugairi
Image caption Ahmed Al-Shugairi, Malami ne mai sassaucin ra'ayin addini.

Ahmed Al-Shugairi Malami ne mai sassaucin ra'ayin addini.

Ya shahara ne bayan ya kaddamar da wani shirinsa a gidan talabijin shekara goma da suka wuce.

Al-Shugiairi ya yi tafiye-tafiye daga wannnan kasa zuwa waccan, inda ake nuna shi a hotunan bidiyo sanye da jamfa da wando, yana jawabi a kan Musulinci.

Irin ra'ayoyinsa na sassauci da zamananci sun sa miliyoyin matasa suna kaunarsa .

Kuma da yake yawanci matasa sun mayar da hankali wajen amfani da shafukan zumunta, shi ma ya mayar da hankalinsa a can inda yake watsa irin manufofinsa na addini, lamarin da ya sa ya zama mai matukar fada-a-ji a shafukan.

Duk da yake ba ya son a rika kiransa da sunan Malamin addini, amma ana kallon Al-Shugairi a matsayin shahararren malami mai sassaucin ra'ayi.

Sai dai masu sukar Malamin mai shekara 42 a duniya suna cewa abin da ya bambanta shi da sauran malamai kawai shi ne tsarin yin wa'azinsa, ba manufar addinin ba.

3. Salman Al-Odah
Image caption A baya ya yi kaurin-suna wajen tsattsauran ra'ayi da adawa da gwamnati.

Salman Al-Odah fitaccen Malamin addini ne a kasar Sudiyya, wanda a baya ya yi kaurin-suna wajen tsattsauran ra'ayi da matukar adawa da gwamnati.

Sai dai ya sauya ra'ayinsa bayan daurin da aka yi masa na shekara biyar a shekarar 1994.

Ana yi masa kallo a matsayin Malamin da ya 'sauya' ra'ayinsa kuma mutane da dama sun ce ya sauya ra'ayinsa ne cikin gaggawa.

Amma duk da haka, wasu lokutan yana tayar da jijiyoyin wuya kan wasu batutuwa.

A shekarar 2012, Al-Odah ya tayar da husuma a shafukan intanet bayan an nuna shi a wani hoto a bayan wani matukin babur lokacin aikin Hajji a Makkah, inda yake kokarin kaucewa cunkoson abubuwan hawa, kuma ana ganin bai dace

Malami kamar sa ya yi hakan ba.

Ya yi matukar fice wajen amfani da shafukan sada zumunta, kuma ba ya tsoron bayyana ra'ayoyinsa da kuma ganawa da miliyoyin masu mu'amala da shi a shafukan.

A wani sakon Snapchat da ya aike wa masu bibiyarsa a shafukan zumunta, Al-Odah ya bayyana cewa ya kamata maza su auri mace guda kawai, lamarin da ya jawo cece-kuce a kasar da ta amince da auren mata hudu.

Al-Odah ya dade da nisanta kansa da tsattsauran ra'ayi da kuma masu tayar da zaune-tsaye.

A lokacin da aka cika shekara shida da kai harin Ranar 11 ga watan Satumba a Amurka, ya gabatar da wata huduba inda yi kakkausan suka kan shugaban Al-Qaeda Osama bin Laden.

4. Nawal Al-Eid
Image caption Nawal Al-Eid tana daya daga cikin mata masu wa'azin ta shafukan sada zumunta

Nawal Al-Eid tana daya daga cikin masu wa'azin da suka fi yin amfani da shafukan sada zumunta a Saudiyya.

Wata mujallar kasar ta zabe ta a matsayin macen da ta fi shahara a shafukan sada zumunta a kasar.

Al-Eid ba ta taba sanya hotonta a shafinta na sada zumunta ba.

Ko da ya ke tana koyarwa a Jami'ar Riyadh, Al-Eid ta fi yin suna a wani shirin gidan rediyo da take gabatarwa a kan 'yancin mata.

Ra'ayoyinta sun sha tayar da jijiyoyin wuya a kasar.

Al-Eid tana matukar adawa da masu karbar akidojin kasashen turai. Ta yi amannar cewa yin biyayya ga dokokin Musulinci zai bai wa mata damar samun 'yancin kansu.

A wata Makala da ta wallafa, Al-Eid ta yi suka kan matan da ke son a basu 'yanci daidai da na maza.

Ta tambaya cewa, "Shin jikin mata zai iya jurewa irin wahalhalun da maza ke sha"?

Blog by Faisal Irshaid, Ahmed Nour Additional reporting and illustrations by Mai Noman