An hana sayar da kilishi a Borno

Image caption Matsalar satar shanu ta addabi arewacin Najeriya

Gwamnatin jihar Borno ta hana shigar da shanu daga yankunan kananan hukumomin jihar.

Gwamnatin ta ce ta dauki matakin ne domin ta gano wasu bata-garin dillalai na hada baki da ‘yan Boko Haram wajen satar shanun a sayar wa jama’a.

Ana kuma zargin suna amfani da kudaden da suka samu daga sayar da shanun satar, wajen gudanar da aikace-aikacen Boko Haram.

Gwamnan jihar Borno Kashim Shettima ya ce daga yanzu za a kara sojoji a kan fararen hula wurin kula da gudanar da harkoki a kasuwar sayar da shanu da ke Maiduguri.

Har ila yau kuma gwamnan ya hana sayar da Kilishi.

Kazalika, ya tsaurara matakai a gidajen yankan dabbobi.