Manyan attajiran Nigeria sun boye $20bn —CBN

Hakkin mallakar hoto Nigeria State House
Image caption Naira na ci gaba da faduwa sakamakon karancin Dala.

Shugaban babban bankin Nigeria, Mista Godwin Emefiele, ya ce wasu hamshakan masu kudin kasar sun boye kimanin Dala biliyan 20 a bankunan kasar daban-daban.

Mista Emefiele ya ce boye kudaden ne ya janyo matsalar karancin dalar Amurka da ake fuskanta a Nigeria, lamarin da ya sa darajar Naira ke ci gaba da faduwa.

Gwamnatin kasar dai ta kayyade Dala daya a kan Naira 197, sai dai a kasuwar musayar kudaden waje ta bayan-fage ana sayar da kowacce Dala daya a kan fiye da Naira 325.

Shugaban babban bankin ya ce wasu 'yan kasar masu muguwar aniya ce ke boye Dalar da zummar ci gaba da samun kudi ta mummunar hanya.

Karancin Dalar dai ya sanya tattalin arzikin Nigeria ya fada cikin mawuyacin hali.