Nigeria: wahalar mai ta ta'azzara

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Dogayen layukan mai ya tilastawa masu motoci sayen mai a wajen 'yan bunburutu.

Matsalar karancin man fetur a Najeriya, ta na kara ta'azzara, abin da ke jefa masu abubuwan hawa cikin mawuyacin hali.

A wasu wuraren ciki har da Abuja babban birnin kasar, mutane kan shafe kwanaki biyu a kan layi a gidajen mai kafin su kai ga samun man, a yayin da wasu kuma suka gwammaci saye a wurin 'yan bumburutu.

Bayanai sun ce haka lamarin yake a sassa daban-daban na kasar, musamman ma a cikin manyan biranen inda akwai dimbin ababen hawa.

Sai dai kamfanin man fetur na kasar, NNPC, ya ce matsalar ta samo asali ne sakamakon gibin da aka samu wajen samar da man a sanadiyar fasa bututan mai, da kuma jinkirin shigowa da tataccen man daga kasar waje.

Kakakin kamfanin na NNPC, Mista Ohi Alegbe, ya kara da cewa nan ba dadewa ba, za a magance matsalar, kana man zai wadata a gidajen mai.