Zika na lalata kwayoyin halittar kwakwalwa

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Kwayar cutar Zika na lalata kwakwalwa

Masu bincike sun ce sun gano yadda kwayar cutar Zika ka iya lalata kwayoyin halittar da ke cikin kwakwalwar 'yan tayi.

Masana kimiyya a Amurka sun ce kwayar cutar ta na kashe kwayoyin halittar kwakwalwa, inda hakan kan haifar da a haifi yaro da tawaya ko kuma dan karamin kai.

To sai dai kuma binciken bashi da nasaba da cutar Zika da kuma haifar yara masu nakasa.

Hukumar lafiya ta duniya wato (WHO) ta ce akwai shaidar da ke nuna irin illar da cutar ta Zika ke da ita, a saboda haka ne ta kira wani taron gaggawa wanda za a gudanar a cikin mako mai zuwa domin tattauna yadda za a yaki zutar ta Zika.