Ana ci gaba da kidayar kuri'u a Benin

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Daya daga cikin magoya bayan wani dan takara a zaben ke nan, a in da ya zane jikinsa da launin gwaninsa.
Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Wani magoya bayan dan takara ke nan ke tallar gwaninsa a yakin neman zaben.

An rufe rumfunan zabe a Jamhuriyar Benin a in da mutane 33 ke takarar neman shugabancin kasar.

Shugaba mai ci Boni Yayi na shirin sauka bayan ya yi wa'adi biyu ya kuma yi aniyar mika mulkin ga wanda ya samu nasara.

Kundin tsarin mulkin kasar ya haramta wa Shugaban yin tazarce, ko da ya ke ya taba yunkurin yin hakan na dan wani lokaci.

Samar da aikin yi da kuma yaki da cin hanci da rashawa na daga cikin manyan alkawururrukan da 'yan takaran ke yi wa masu zabe.

Masu kada kuri'a sama da miliyan talatin aka yi wa rajista sai dai an samu wasu da suka yi korafin cewa ba su ga sunnayensu a cikin rajistar ba.