Shirin Dadin Kowa ya ci kyauta

Hakkin mallakar hoto Salisu Balarabe
Image caption Salisu Balarabe tare da 'yan wasa da kuma ma'aikatan shirin Dadin kowa a yayin daukar shirin

Shirin wasan kwakwaiyo na Dadin Kowa shi ya lashe gasar fina-finai da wasannin kwaikwayo na talbijin da aka yi da Hausa na shekarar 2016.

Dadin Kowa wasan kwakwayo na talbijin ya doke fim din Sarki Jatau da Sakaina da Baya da kura da kuma In ji 'yan caca.

Gasar wadda ake yi duk shekara gidan talbijin na Magic Africa ne ke shirya shi, in da masu kallo ke zaben wasan Hausan da ya fi burgesu ta hanyar intanet.

Mai shirya shirin Dadin Kowa Salisu Balarabe tsohon mai shiryawa da ba da umarni ne a kannywwood, kuma ma'aikaci a gidan talbijin na Arewa24 wanda ke daukar nauyi da kuma nuna shirin.

Ga karin bayanin da Salisu ya yi wa Yakubu Liman a kan wasan kwaikwayon, da kuma dalilin da ya sa ya ci kyautar.

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti